Coronavirus
Sama da ‘yan Najeriya 500,000 ne aka yiwa riga-kafin Corona – Gwamnatin tarayya
Hukumar lafiya matakin farko ta ce a yanzu haka sama da mutane dubu dari biyar ne aka yiwa riga-kafin Corona a Nigeria.
Hukumar ta kara da cewa mutane dubu dari biyar da goma sha uku da dari shida da ashirin da shida aka yiwa riga-kafin a jihohi 35 dake kasar nan har ma da birnin tarayya Abuja.
A cikin kiddigar da hukumar ta fitar ya nuna cewa, jihar Kogi ce har yanzu ba a fara yiwa allurar riga-kafin ba duk da cewa cutar ta kama sama da mutane dubu dari da sittin da biyu a kasar nan.
Shugaban hukumar Faisal Shuaib ya ce dalilin da ya sa alluarar ba ta isa jihar ta Kogi ba shine saboda dakin da ake ajiye na’uwar dake sanyaya allurar ya sami matsala a lokacin zanga-zangar EndSARS.
Wata kididdiga ta nuna cewa Jihar lagos ce kan gaba a wadanda suka kamu da cutar ta Corona wadda a yanzu haka aka yiwa al’ummar jihar riga-kafi dubu dari da goma da Arba’in da biyu, sai jihar Ogun wadda aka yiwa al’ummar jihar riga-kafi dubu arba’in da bakwai da dari biyar da bakwai.
Sauran sune jihohin Kaduna wadda aka yiwa mutane dubu 38,063 yayin da Katsina aka yiwa mutane 28,918 sai kuma jihar kwara da ka yiwa 26,473.
You must be logged in to post a comment Login