ilimi
Sama da yara miliyan 10 ne basa zuwa makaranta a Najeriya – Adamu Adamu
Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwar ta kan yadda ake samun karuwar yaran da basa zuwa makaranta a kasar nan.
Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ne ya bayyana hakan lokacin da yake fitar da adadin yaran da ba sa zuwa makaranta wanda adadin su ya kai miliyan 10 a yanzu.
Wannan dai na nuna yadda adadin yaran da basa zuwa makaranta ya karu daga miliyan shida da dubu dari tara da arba’in da shida zuwa milyan goma daga shekarar da ta gaba zuwa yanzu.
Idan za a iya tunawa ministan Ilimi Adamu Adamu, a farkon wannan Janairun shekarar da muke ciki ya ce yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a shekarar 2019 ya kai miliyan 10 da dubu dari daya, adadin da ya nuna ana samun raguwar matsalar a shekarar 2020 da a lokacin aka da yara sama da miliyan shida.
Nwajiuba ya ce har yanzu an gaza gano dalilan da ke janyo karuwar yaran da basa zuwa makaranta, sai dai ya ce Najeriya za ta magance wadannan kalubalen yadda ya kamata, ta hanyar inganta ilimin firamare.
You must be logged in to post a comment Login