Labarai
Samar da yan sandan jihohi zai kawo karshen matsalar tsaro –ALGON

Shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya ALGON, Kolade Alabi, ya sake nanata bukatar samar da ‘yan sandan jihohi.
Shugaban yayi wannan kira ne lokacin da ya jagoranci kwamitin zartarwa na kungiyar a wata ziyarar jaje da suka kai wa gwamnan jihar Naija Abubakar Sani Bello.
A cewar Alabi, za a iya shawo kan kalubalen tsaro a yanzu idan aka samar da ‘yan sandan jihohi a kasar nan, domin kuwa za su iya kawo karshen ayyukan yan tada kayar baya a yankunan su.
Alabi ya yi kira da a kara wa jihohi da kananan hukumomi kaso don magance kalubalen abubuwan more rayuwa da kuma gazawar tsaro
You must be logged in to post a comment Login