Labaran Wasanni
Samir Nasri ya yi murabus daga kwallon kafa
Tsohon dan wasan kwallon kafa na Faransa (France ), Samir Nasri, ya sanar da yin murabus daga Kwallon kafa.
Mai shekaru 34, tsohon dan wasan tawagar Marseille da Manchester City, ya sanar da yin murabus din a tashar Talabijin ta CANAL + ,dake kasar sa ta Faransa.
Dan wasan ya koma tawagar Arsenal a shekarar 2008,daga Kungiyar Marseille wacce ya fara wasannin sa tun daga matakin kungiyar matasa.
Afrobasket: D’Tigress ta kai zuwa wasan karshe
Nasri ya lashe gasar Firimiya sau Biyu da Kofin EFL sai Community shield a Lokacin da yake wakiltar Manchester City.
Dan wasan ya katse Kwantiragin sa da tawagar Antalyaspor ta kasar Turkiyya a shekarar 2018, biyo Bayan samun sa da Laifin Shan magani mai dauke da sinadaran Kara Kuzari da aka haramtawa ‘yan wasa amfani dasu, da hukumar WADA tayi.
“Abu Daya da ba zan taba mantawa dashi ba shi ne zargin amfani da kwaya da na sha musanta cewar ba haka ta kasance ba da hakan ya sa gaba daya na tsani kwallon kafa”.
“Na dauki Lamarin rashin Adalci , saboda nasan banyi wani abu da ya saba ka’ida ba , kuma hakan ya zare mun shaawar wasa kwata kwata” inji Samir Nasri.
You must be logged in to post a comment Login