Labarai
Sana’a ga matasa zai taimaka wajen dakile fadan daba da shaye-shaye ga matasa- Kungiya
Ƙungiyar masu ƙere-ƙere da sarrafa kayayyakin abinci da kuma masu bincike don gano ilmin da zai amfanar da al’umma ta CONERSEN a Kano, ta ce riƙo da ƙananan san’o’in hannu ga matasa shi ne zai magance matsalar shaye-shaye da faɗan Daba, tsakanin matasa a jihar nan.
Shugaban ƙungiyar Turakin Wazirin Kano Mallam Ɗahiru Sa’idu Giɗaɗo ne ya bayyana hakan, yayin taron bajakolin fasahar masu ƙananan san’o’i da basu shawarwari ta yadda zasu ƙara samun ƙwarin Gwiwa a harkokinsu, wanda ya gudana jiya Laraba.
A cewar sa lokaci ya yi da ya kamata matasa su farka daga bacci tare da zage damtse wajen neman na kan su.
Wasu daga cikin matasan da suka halarci taron bajakolin sun bayyana godiyarsu ga wannan kungiyar, wadanda suka ceirin wadannan tarukan zas taimaka wajen karawa masu kananan sana’o’i gwiwa, dama sa wadanda basu da sana’o’in su fara.
Taron wanda ya gudana a ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jihar Kano ya samu halattar manyan mutane daban-daban da ƙwararru ciki har da babban Jakadan Burtniya, a kasar nan.
Rahoton: Abdukadir Haladul Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login