Kasuwanci
Sarki Aminu Ado Bayero ya bukaci a rungumi tsarin eNaira da Cashless Policy
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jaddda goyon bayansa ga tsarin eNaira da tsarin takaita hada-hadar tsabar kudi a hannun al’umma wadanda babban bankin Nijeriya CBN ya kirkiro da su domin magance matsaloli da kuma hatsarin yawo da tsabar takardun kudi a hannu.
Sarkin ya bayyana goyon bayan nasa ne yau Talata lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar banakunan Nijeriya karkashin jagorancin Daraktan a babban bankin CBN shiyyar Kano Alhaji Muhammad Hamisu Musa da suka ziyarci Sarkin a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce tsarin na eNaira da kuma na takaita hada-hadar tsabar kudi a hannun mutane suna tamaka wa yan kasuwa da sauran al’ummar kasa baki daya.
Haka kuma Sarkin, Ya CNB da ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gyara matsalar karancin sadarwa da al’umma ke fuskanta yayin aikewa ko kuma hada-hadar kudi ta asusun bankuna.
A nasa jawabin Daraktan a CBN Alhaji Muhd Hamisu Musa, ya ce, sun kai ziyara fadar Mai martaba Sarkin na Kano ne domin shaida masa irin hanyoyin da suke bi wajen wayar da kan al’umma amfanin tsarin na tsarikan na takaita amfani da tsabar kudi musamman ga ‘yan kasuwar jihar Kano domin taimaka wa musu ta fuskar kara habbaka kasuwancinsu.
Alhaji Muhd Hamisu Musa, ya kara da cewa, suna shiga har cikin Kasuwanni domin zama da ;yan kasuwa da sauran al’umma tare da wayar musu da kai wajen ganin sun fahimta tare da karbar tsarikan bisa irin tarin alfanun da suke da shi.
You must be logged in to post a comment Login