Labarai
Sarki Aminu Ado ya bukaci a rika dasa bishiyoyi don dakile kwararowar Hamada
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci shugabanin kananan hukumomin jihar da su rika taimaka wa makaratun yankunansu da dashen bishiyoyi domin kare kwararowar Hamada.
Sarkin ya bukaci hakan lokacin da ya karbi bakoncin shugabar kungiyar dashen bishiyoyi da kare kwararowar Hamada ta Green Enviromental Solution Hajiya Ummi Tanko Yakasai, da ta ziyarce shi a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kuma ce, dashen bishiyoyi na da matukar mahimmanci duba da yadda ake samun wasu mutane na sare bishiyoyi ba bisa ka’idaba.
A nata jawabin, shugabar kungiyar ta Green Enviromental Solution Hajiya Ummi Tanko Yakasai, ta ce, ta kai ziyarar ne domin neman sanya albarkar Sarkin bisa irin ayyukan da suke yi na dasa bishiyu a makarantu.
Track up
Shugabar kungiyar ta kara da cewa zuwa lokacin da suka ziyarci fadar Sarkin, sun samu nasarar dasa bishiyoyi fiye da dubu daya a makarantun Firamare.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login