Labarai
Sarki Sunusi ll ya bukaci mutane su rika yin koyi da halayen magabata

Mai martaba sarkin kano khalifa Muhammadu Sunusi ll, ya bukaci al’ummar jihar da su rika yin koyi da kyakkyawan halayen magabata da suka bayar da gagarumar gudunmawar wajen ciyar da jihar Kano gaba.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da littafi mai taken Musan magabatanmu wanda Injiniya Kabiru Ahmad Kwalli ya wallafa Kan irin gagarumar gudummawar da wasu fitattun mutane a jihar nan suka bayar wajen ciyar da Kano gaba wanda aka gudanar a dakin taro na jami’ar North West dake nan kano.
Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya yaba da kokarin mawallafin littafin bisa ga hangen nesa da yayi wajen zakulo mashahuran mutane wadanda suka bada gudummawa a fannoni daban daban na rayuwar Jama’a.
A nata jawabin shugabar jami’ar ta North West Farfesa Amina Salihi Bayero, ta ce littafin zai taimaka musamman ga yara masu tasowa wajen sanin magabata da suka bada gagarumar gudunmawa wajen hidimtawa al’umma dama kasa baki daya.
Taron, ya samu halartar Farfesa Ibrahim Garba Satatima da Farfesa Abdallah Uba Adamu da Malam Ibrahim Khalil inda suka gabatar da mukala.
You must be logged in to post a comment Login