Connect with us

Labarai

Kotu ta umarnin kai mata hujjojin shari’ar Malam Abduljabbar

Published

on

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci kotun da ta yanke wa Malam Abduljabbar Nasir Kabara, hukuncin kisa da ta gabatar mata da littattafan da aka yi amfani da su a matsayin hujjoji yayin gudanar da shari’ar.

 

A zaman kotun na yau Litinin, alkalan kotun ƙarƙashin jagorancin Nasir Saminu da Sanusi Ado Ma’aji, sun saurari ɓangarorin da ke ƙara da waɗanda ake ƙara.

 

Tun da farko an ba ɓangaren waɗanda ake ƙara damar gabatar da martaninsu, kuma a yau sun yi hakan. Kotun ta saurari bayanan kowane ɓangare tare da karɓar hujjojinsu.

 

Haka kuma, kotun ta umarci a gabatar mata da littattafan da Malam Abduljabbar ya yi bayani a kansu yayin shari’ar, tare da bayyana cewa za ta sanar da ranar yanke hukunci nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!