Labarai
Sarkin Gaya ya bukaci matasa da dalibai su guji tu’ammali da miyagun kwayoyi

Mai martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Abubakar ya yi kira ga matasa da su dalibai dasu guji yin ta’ammali da miyagun kwayoyi tare da sanya ido a kayan da gwamnati ta samar musanman a fannin ilimi
Sarki n ya bayyana hakane a lokacin da kungiyar dalibai ta kasa rashen karamar hukumar gaya suka kai masa ziyara a fadarsa
Sarkin na Gaya ya kuma ja hankalin kungiyar daliban da su jajirce wajen neman ilimi domin shine ginshikin rayuwa, haka kuma sarkin ya hori daliban dasu guji shaye shaye da fadan daba don kyautata rayuwarsu.
Daya ke jawabi shugaban kungiyar daliban, Bello Abdullahi Torenke yace makasudun ziyarar shine neman tabariki da kuma ban girma ga mai martaba sarki.
Sarkin gaya dakta Aliyu Ibrahim ya godewa kungiyar daliban bisa wannan ziyara ,tare da yi musu addu’a da fatan alheri.
You must be logged in to post a comment Login