Labarai
Dangote ya kara farashin mai zuwa Naira 1,275 kan kowacce lita

Dangote ya kara farashin mai zuwa N1,275 tare da dakatar da sayarwa na wucin gadi
Matatar Dangote ta kara farashin man fetur (PMS) zuwa N1,275 kan kowace lita, daga N1,200, lamarin da ke kara fargabar tashin farashin mai a fadin kasar.
Rahotanni sun kuma nuna cewa matatar ta dakatar da sayar da mai na wani dan lokaci sakamakon matsala a tsarin Proforma Invoice, wanda ya shafi jigilar kaya.
Wannan mataki ya janyo damuwa a kasuwar man fetur, inda ‘yan kasuwa ke hasashen karin farashin mai a gidajen mai a sassan kasar.
You must be logged in to post a comment Login