Labarai
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne shugaban majalisar sarakuna – Ganduje
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan dokar da ya yiwa gyaran fuska ta masarautu inda ta tabbatar da Sarkin Kano Alhaji Aminu AdoBayero a matsayin shugaban majalisar sarakuna maimakon tsarin karba-karba.
Gwamna Ganduje ya sanya hannun ne a yau ya yin taron majalisar zartarwa a fadar gwamnatin Kano
Ganduje ya Kara da cewa saboda muhimmancin Masaurautar Kano da take ta hudu a Nigeria wanda ba’a son samun yanayin da za’a hana ko dakatar da Sarkin na Kano shiga taron shugabannin hukumomin sarakuna na kasa, adon hakane a ka mayar da shugabancin na din -din akan sarkin Kano.
A cewar dokar ta kuma kara adadin masu zaben sarki daga mutum hudu zuwa mutum biyar.
Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa a ya yin taron majalisar zartarwar an kuma sanya hannu akan dokar da ta bada damar kafa hukumar masu bunciken kayayyaki da kudade a dukkan ma’aikatun gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login