Kiwon Lafiya
Sarkin Kano ya bukaci ‘yan kasuwar Najeriya su kara kaimi wajen jera kafada da takwarorinsu na kasashen ketare wajen fitar da kayayyakin da suke sarrafawa
Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga cibiyar hadin gwiwa ta kasuwanci ta Najeriya da Habasha da ta kara kaimi wajen jera kafada da wasu kasashen da suka jajirce wajen fitar da kayayyakin su da suka sarrafa a gida zuwa wasu kasashen, domin inganta kamfanonin da suke sarrafa kaya a cikin gida.
Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin tawagar mambobin cibiyar da suka kai masa ziyara fadar sa, karkashin jagorancin shugaban cibiyar na kasa Alhaji Umar Abdulkadir Dangote.
Malam Muhammadu Sanusi II ya kuma bukaci cibiyar kasuwancin ta Najeriya da kuma Habasha da suyi dukkan mai yuwuwa wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba, ta hanyar bunkasa masana’antun Najeria.
Da yake jawabi, shugaban cibiyar Alhaji Umar Abdulkadir Dangote ya ce sun je fadar ne domin sanarwa Sarkin irin shirye-shiryen da cibiyar take yi wajen hada kai da sauran kasashe kan batun fitar da kayayyakin da aka sarrafa daga cikin gida zuwa kasashen ketare.
Haka zalika mai martaba Sarkin na Kano ya kuma nada Alhaji Muhammad Aminu Umar a matsayin dagacin garin Wantum da ke yankin karamar hukumar Warawa.