Labarai
Sarkin Kano ya umarci Hakimai da Dagatai da Limamai su dage da addu’o’in samun tsaro

Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi ll, ya umarci Hakimai da Dagatai da masu unguwanni har ma da Limaman masallatan Juma’a da su dage da addu’o’in samun zaman lafiya a jihar Kano da ma Najeriya baki daya.
Sarkin ya bada umarnin ne ganin yadda wasu mahara suka shiga karamar hukumar Shanono inda kuma yawan addua’r da ake yi ya sanya aka samun nasara kashe 19 daga cikin ɓata garin.
Mai martaba sarkin ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa tura sojoji da jami’an tsaro na DSS yankin farin a kan lokaci.
Sarkin ya kuma ce, addu’a kadai ce za ta kawo karshen maharan.
You must be logged in to post a comment Login