Labarai
Sarkin Kano ya yi suka kan yadda siyasa mallakar dukiya ta hanyar ya ki Halak ya ki Haram

Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi, ya soki yadda shugabancin siyasa a Najeriya, ke rikidewa daga hanyar ci gaba zuwa mallakar dukiya ta hanyar yaki halal yaki haram.
Sanusi ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru 15 na Enough is Enough Nigeria a birnin Lagos, inda ya ce rashin cigaba yana faruwa ne saboda shugabanni na fifita kansu da masoyansu fiye da bukatun al’umma.
Jaridar Daily Trust ta ambato shi ya na jaddada cewa kasar mallakar kowa ce, ba gwamnati ba, kuma kowa na da hakkin bayar da gudummawarsa wajen ci gaban ta wajen ginuwarta, ba tare da nuna wani banbancin kabila ko addi ba.
You must be logged in to post a comment Login