Manyan Labarai
Sarkin Kano yace zai cigaba da kare mutuncin masarauta
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya ce za suyi duk mai yiwuwa wajen kare kima da mutuncin masarautar Kano da ma al’ummar jihar Kano baki daya.
Muhammadu Sanusi na ya bayyana hakan ne yayin gudanar da addu’ar cika shekara 5 da rasuwar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da kuma murnar ciki shekara sa shekara biyar da zaman sa Sarki da ya guda da safiyar yau a babban masallacin juma’a na Kano.
Sarkin ya ce ya zama wajibi al’ummar jihar Kano su ba da ta su gudunmowar wajen ganin an inganta al’amuran tarihi da na gargajiya da aka gada kaka da kakan ni.
Muhammadu Sanusi na biyu ya a shekara biyar din da ayi yi kan karagar mulki an fuskanci kalubale da dama a jihar kano da ma arewacin kasar nan baki daya, amma cikin ikon Allah an samu waraka.
Sarkin Sanusi yin kira ga daukacin malaman addini da shugabanni a dukkan matakai da su maida hankali wajen hada kansu, tare da yiwa jihar Kano dama kasa baki daya addu’ar zaman lafiya.