Kiwon Lafiya
Sarkin Katsina ya bukaci gawamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa don magance tserewar da manoma da makiyaya
Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yi kira ga gawamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin magance tserewa da manoma da makiyaya ke yi a jihar ta Katsina sakamakon kashe-kashen ‘yan bindiga da kuma masu satar mutane suna garkuwa da su.
Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bayyana hakan ne lokacin da ministan noma Audu Ogbeh da gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefile suka kai masa ziyarar ban girma a fadar sa da ke garin na Katsina.
Ya ce, minista Audu Ogbeh, ’’idan ka koma Abuja ka gayawa shugaban kasa a kula sosai da lafiyar jama’ar mu, musamman wajen tabbatar da tsaron lafiyar su, domin kuwa wadannan shirye-shirye masu kyau da muhimmanci da gwamnati ke kaddamarwa ba zasu samu nasara ba matukar manoma basu da cikakken tsaro’’.
Sarkin na Katsina ya ce kusan kullum sai ya samu labarin an kashe wani ko kuma an sace mutane an yi garkuwa da su daga kauyuka da dama da ke jihar.
Tun farko dai minista Audu Ogbeh da gwamnan na CBN Godwin Emefiele sun je jihar ta Katsina ce domin kaddamar da shirin fara rabon irin Auduga dan wuri ga manoma.