Labaran Kano
Sarkin mayun boge ya karyata kansa
Sarkin mayun nan na boge da aka kama mazaunin garin Albasu bisa zargin dorawa mutane shairrin maita, ya bayyana cewa maitar tasa ta karya ce, domin ‘yan dabaru yake yi da nufin neman kudi.
Wanda yake kiran kansa a matsayin sarkin mayun mai suna Yahaya wanzan ya karyata kansa ne da tsakar ranar jiya Laraba bayan da hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama shi.
Bayan hukumar ta bincike shi ta kuma mayar da shi garin domin ya yi cikakken bayani a gaban mutanen da ake zargin ya damfare su kudade.
Yahaya wanzan dai a baya ya zama wani mashahurin maye a garin na Albasu da yake karbar makudan kudi a hannun mutanen garin domin ya basu magani, sai dai mutane da dama sun fuskanci tsangwama daga gare shi ta hanyar cin zarafinsu.
Da yake jawabi a gaban mutanen, Yahaya wanzan ya nemi yafiyar mutanen garin inda ya kara da cewa, daga yanzu sunansa Yahaya karamin Wanzan a maimakon sarkin Mayu.
A nasa bangaren, Chiroman Mayu na jihar Kano ya karyata maganar Yahaya wanzan na cewa maita karya ce, yace maita gaskiya ce saboda sun gaje ta ne tun iyaye da kakanni.
Da yake tona asirin wasu daga cikin manyan garin da ke mara masa baya wajen karbar kudi daga hannun mutane, ya ce akwai wasu manyan mutane uku a fadar hakimin garin da suka hada da sakataran hakimi da wakilin hakimi da wani mai suna Iliyasu da suke karbar makudan kudade suna bashi damar gudanar da hakar ta sa.
Haka kuma sarkin mayun na boge, ya nemi afuwar mutanen da ya zalinta musamman ma wasu mata biyu da ya ce, ya kaga musu sharrin maita kuma ya umarce su da su yi tsarki su baiwa wasu da ake tunanin mayu sun kama su, wata daga cikin wadanda sarkin mayun ya yaudara ta ce baza ta yafe masa ba, saboda ya janyo mata bakin jini da ita da mijinta da “ya “yanta har ma mahaifiyarta.
A nasa jawabin, shugaban hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, dole ne fadawan su gurfana a gaban hukumar dumin su fuskanci hukunci.