Kiwon Lafiya
Sarkin musulmi na uku ya bukaci yan siyasa da su kaucewa kalaman batanci
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya ja hankalin ‘yan-siyasar Jihar Kaduna da su kaucewa yada kalaman batanci da kiyayya, a maimaikon hakan su mayar da hankali bunkasa harkokin Siyasa gabanin zaben badi.
Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a jiya Talata a Kaduna, lokacin da ya ke jawabi yayin taron lakca da kungiyar Jama’atul Nasril Islam JNI ta shirya domin fadakar da jama’a dangane da karatowar watan Azumin Ramadana.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce abin takaici ne matuka irin yadda wasu ‘yan-siyasa a Kaduna ke furta kalamai ba tare da sanyawawa bakinsu linzami ba, a don haka ma ya nuna rashin jin dadinsa a kan batun.
Sannan ya yi kira a dauki matakan da suka dace wajen kawar da yada kalaman batanci da kiyayya a shafukan zumunta na zamani duba da tasirin hakan ka iya haifarwa a Jihar ta Kaduna dangane da rikicin addini da Siyasa.
A karshen makon jiya ne dai aka jiyo gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ayyana ‘yan Majalisar dattijain guda uku a matsayin marasa amfani kuma wadanda basa kaunar ci gaban Jihar ta Kaduna.
Jawabin na El-Rufa’i na da nasaba da kin amincewa da Majalisar dattijai ta yi ga yunkurin gwamnan na karbo rancen kudi domin gudanar da ayyukan raya kasa a Jihar, bayan da Sanata Shehu Sani da Sulaiman Hunkuyi da Danjuma Laah suka nuna tirjiyarsu a fili ga bukatar El-Rufain.