Connect with us

Labaran Wasanni

Saudi Arabia ta kawo karshen wasanni 36 da Argentina ke samun nasara

Published

on

Tawagar kwallon kafar kasar saudiya ta doke kasar Argentina a wasan farko na gasar cin kofin duniya a kasar Qatar da ci biyu da daya a yau Talata a rukuni C.

Kyaftin din tawagar Argentina Lionel Messi ne ya fara saka kasar tasa a gaba, a bugun daga kai sai mai tsaron raga a mintuna na goma.

Sai dai mintuna uku bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kasar ta Saudia ta warware kwallon ta hannun Al- Shehri kana dan wasa Al-Dawsari ya zura kwallo ta biyu a minti na 53 wanda hakan ya basu  nasarar farko a gasar ta bana.

Kasar ta Argentina na cikin jerin kasashen da ake saka ran zasu lashe gasar ta Duniya a bana.

Wannan shi ne karon farko da kasar ta saudia ta samu nasara a wasan ta na farko.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!