Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Saura ƙiris na shawo kan waɗanda ba su amince da Abdullahi Abbas ba – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, shalkwatar Jam’iyyar APC ta ƙasa ta amince da Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaban ta a Kano.

Gwanduje ya faɗi hakan gabanin fara taron majalisar zartarwa ta jiha a ranar Laraba.

“shalkwatar Jam’iyyar ta ƙasa ta amince da zaɓen da muka yi wa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban Jam’iyyarmu na jiha”.

Ya ci gaba da cewa “Uwar jam’iyyar ta amince da duk shugabannin da aka zaɓa lokacin da Abdullahi Abbas ya yi nasara”.

“Saura ƙiris na shawo kan waɗanda ba su amince da Abdullahi Abbas ba, domin kuwa hakan zai sa a samu ci gaba” in ji Ganduje.

Abdullahi Abbas ne halastaccen shugaban jam’iyya a Kano – APC

Gwanduje ya kuma ce, duk da haka akwai yunƙuri na yin sulhu da wasu tsiraru da suka bi wata hanya, don ciyar da harkokin siyasa gaba.

Wannan dai na cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa Labarai na gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya fitar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!