Connect with us

Labarai

Sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatina ke aiwatarwa sun jefa talakawa cikin wahala- Shugaba Tinubu

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu,  ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun jawo wa ‘yan Najeriya wahala, yana mai cewa shi ma ya rasa barci da kuzari da ya tilasta masa ramewa da kuma shiga matsananciyar damuwa sakamakon matsin rayuwar da ake ciki.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin karbar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC  domin zaben shekarar 2027.

Tinubu ya ce yana sane da radadin da jama’a ke ciki sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki da aka fara tun bayan hawansa mulki, amma ya jaddada cewa dole ne ya ci gaba da aiwatar da su domin gyara kasar.

Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin da kuri’u 10,999,162, inda ya kayar da abokin takararsa guda daya, Stanley Osifo, wanda ya samu kuri’u 16,503.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!