Labarai
SERAP ta maka Kamfanin NNPCL a gaban kotu

Kungiyar rajin tabbatar da adalci ta SERAP, ta shigar da ƙara a kotu kan Kamfanin man fetur na kasa NNPCL, bisa zargin kasa yin cikakken bayani kan wasu kuɗaɗe da suka kai sama da Naira tiriliyan 211 da aka nuna a cikin rahoton binciken kuɗaɗen kamfanin na shekarar 2023.
SERAP ta ce waɗannan kuɗaɗe na cikin rahoton binciken kamfanin na shekarar 2023, a ƙarƙashin rukunin Sauran Kuɗaɗen da ake bin Kamfanin, da kuma Kuɗaɗen da aka tara amma ba a biya ba, ba tare da an yi isasshen bayani da zai ba jama’a damar fahimtar yadda aka gudanar da mu’amalolin ba.
Kungiyar ta ce manufar ƙarar ita ce neman kotu ta umarci NNPCL ta bayyana cikakkun bayanai kan waɗannan kuɗaɗe domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma kare dukiyar al’ummar kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login