Labarai
Babban jami’in kula da harkokin kuɗi na ISWAP ya miƙa wuya ga Sojoji

Rundunar Sojin kasar nan, ta ce wani babban jami’in kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar ISWAP ya miƙa wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a Jihar Borno tare da wasu yara maza biyu.
Mai Magana da yawun rundunar a Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce mutumin ya miƙa wuya ne da misalin ƙarfe 6:45 na safiyar ranar 25 ga Yuli, 2026, a kan hanyar Ladari zuwa Jegarawa a jihar Borno.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa mutumin shi ne ke kula da harkokin kuɗi da samar da kayan aiki ga sansanin ISWAP da ke Jubillaram, kuma ya yanke shawarar miƙa wuya ne sakamakon matsin lambar hare-haren ƙasa da na sama da sojoji ke kai wa ƙungiyar.
You must be logged in to post a comment Login