Connect with us

Labarai

Rundunar Soja ta kama jami’inta da ta ke nema ruwa a jallo

Published

on

Rundunar Sojin Najeriya, ta sanar da kama wani jami’inta Mohammad Yusuf, wanda ta ayyana nemansa ruwa a jallo bisa zargin safarar kayan aikin soja ga ‘yan ta’adda.

Ta cikin wata sanarwa da ta fitar rundunar ta ce an kama jami’in ne a ranar 25 ga Yuli a tashar Jidari da ke Maiduguri, Jihar Borno, bayan bayanan sirri sun nuna cewa yana ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasar Kamaru.

A cewar rundunar Operation HADIN KAI, Yusuf wanda ke aiki a Nigerian Army Ordnance Kits Factory da ke Legas, ya tsere daga sansaninsa tun ranar 7 ga Yuli, sannan ya ɓuya a unguwar Gomari Costain da ke ƙaramar hukumar Jere tare.

 

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadan da ke da hannu a kan lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!