Labaran Wasanni
Shafukan sada zumunta: A kawo karshen cin zarafin ‘yan wasa – Hukumomi
Hukumomin kwallon kafa a kasar Ingla sun bawa shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook damar bada kariya ga ‘yan wasan kwallon kafa da wasu ke amfani da shafukan wajen cin zarafin ‘yan wasan.
Hakan na kunshe cikin wata takarda da wasu daga cikin gamaiyar hukumomin suka aike wada shugabannin dake tafiyar da shafukan Jack Dorsey da Mark Zuckerberg.
Sun kuma tsara ka’idojin da suke bukata a sanya tare da tilastawa masu amfani da shafukan yin biyayya ga ka’idojin don dakile cin zafin ‘yan wasan.
‘Yan wasa da dama ne daga kungiyoyi daban-daban ke ci gaba da fuskantar kalubale ta hanyar aike masu da sakonnin cin mutunci tare da barazana ga rayuwar iyalansu a shafukan sada zumuntar, lamarin da hukumomin ke ganin ya zama dole a dauki kwararan matakai.
A jiya Laraba ne mai tafiyar da Facebook Mack Zuckerberg, ya bayyana tsauraran matakan da zai dauka kan masu amfanin da kafar wajen cin zarafin ‘yan wasa.
You must be logged in to post a comment Login