Labarai
Shaik Gumi ya kara jaddada bukatar yin sulhu da ‘yan ta’adda a Nijeriya
A baya lokacin tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Sheikh Ahmed Mahmud Gumi ya sha yiwa gwamnatin tayin sulhu da ‘yan bindiga amma bai sami karbuwa ba.
Ya kuma ya ce tunda manyan kasa sun sake ta da maganar, wajibi ne a jawo hankalin sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Dr. Gumi ya ce ‘sulhu ba ya nufin gazawar jami’an tsaro a kasar nan amma hanya ce ta magance matsalar tsaro cikin sauki, la’akari da sabuwar gwamnati aka samu to maganar sulhun kan iya yin tasiri’.
Shehin malamin ya kuma yi fatan gwamnatin Bola Tinubu za ta amince tare da yin sulhu da ‘yan binger dan samun tsaro mai dorewa a kasar nan.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login