Connect with us

Labarai

Shara na barazanar rushe mana gidaje- Mazauna Hotoro

Published

on

Mazauna Unguwar Hotoro Ramin Kwalabe a Kano, sun bukaci hukumar kwashe shara da ta kai musu dauki bisa wata tarin shara da mutane ke tarawa a yankin wadda kuma ta ke barazana ga rayuwarsu.

 

A cewar mazauna yankin har ta kai da cewa tarin bolar na yin barazana ga rushewar gidajensu, Kamar yadda suka shaida wa Freedom Radio.

 

Kan wannan koke nasu ne Freedom Radio ta yi kokarin jin ta bakin hukumar kwashe shara ta Kano REMASAB, sai dai hakan mu bai cimma ruwa ba, amma dai za mu ci gaba da bibiyar hukumar domin jin abinda za ta yi kan wannan matsala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!