Addini
Shari’ar Abduljabbar: Kotu ta fara sauraron shaidu
Babbar Kotun shari’ar musulunci dake zamanta a kofar kudu karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ta fara sauraran shaidun da gwamnatin Kano ke gabatarwa kan sheikh Abduljabbar Kabara.
Lauyan gwamnati Barista Mamman Lawan Yusufari ne ya jagoranci lauyoyin, inda kuma Barista Umar Muhammad ya jagoranci lauyoyin wanda ake kara.
Kotu tayi waiwaye inda ta tambayi lauyoyin Malam Abduljabbar ko suna nan a matsayinsu na kin amincewa da cigaba da shari’a sakamakon lauyoyin baya sunki amincewa da cigaba?
Nan take sabon lauyan yace a cigaba, lamarin da ya sanya aka fara gabatar da shaidu biyu.
An gabatar da shaida na farko mai suna Adam Adam mazaunin filin D.O dake Gwale inda ya ce yana zuwa karatun da ake yi a Masallacin As’habul Kahfi da Jami’atur Rasul dake Sabuwar Gandu.
Kotu tasa shi ya yi rantsuwa, sannan lauyan gwamnati ya fara yi masa tambayoyi, inda ya tabbatar da tuhumar da ake yiwa Malamin.
Haka shima lauyan Malamin ya yi masa tambayoyi, inda aka tafi hutu bayan yimasa tambayoyin za kuma a dora idan an dawo.
You must be logged in to post a comment Login