Labarai
Sheikh Balalau yana nan a raye –Pantami

Ministan sadarwa na kasa Dakta Isah Ali Pantami ya karyata rade-radin da ake yadawa na rasuwar shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Balalau.
Jaridar Sahara Reporters ce ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Facebook da tace na jana’izar malamin ne.
Saidai Dakta Pantami yayi tsokaci kan wannnan labari a nasa shafin na Facebook inda yace Sheikh Abdullahi Balalau yana nan cikin koshin lafiya.
A karshe Dakta Pantami yayi fatan jaridar zata gyara wannan labari da ta sanya.
Karin labarai:
Ba muyi nadamar zabar Buhari ba -Izala
You must be logged in to post a comment Login