Connect with us

Labarai

Pantami ya baiwa samari maganin farin jini

Published

on

Ministan sadarwa na kasa Dakta Isa Ali Pantami ya baiwa samari lakanin samun farin jini a wurin ‘yan matansu.

Wani matashi mai amfani da shafin Twitter ne ya roki ministan da cewar “Mallam a taimaka mana da maganin farin jini muma”.

Nan take kuwa sai Malam Pantami ya bashi amsa da cewa “kwatanta bin dokokin Allah da addu’ar iyaye”.

A karshe Malam Pantami yayi addu’ar cewa Allah ya sa mu wanye lafiya.

Minista Pantami dai malamin addinin musulunci ne da yake da farin jini a wurin al’umma a kasarnan.

Da fatan samari za suyi riko da wannan lakani da Malam ya bayar.

Karin labarai:

Sheikh Balalau yana nan a raye –Pantami

Covid-19: Ban san me ya hada 5G da Coronavirus ba – Pantami

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!