Addini
Shekaru 69 da fara Maukibin Kadiriyya
Dubban mabiya darikar Kadiriyya sun yi dafifi a yau Asabar domin gudanar da maukibin Kadiriyyaka karo na 69 wanda aka saba gudanarwa a duk shekara da nufin tunawa da ranar haihuwar Sidi Abdulkadir Jilani.
Maukibin wanda Shugaban darikar Kadiriyya na Afurka Sheikh Muhammd Nasiru Kabara ya assasa lokacin yana raye, ya fara shi ne da mutane 40, a yanzu kuma dubbaI ne ke halartar taron daga jihohin kasar nan da wasu daga cikin kasashen ketare.
Tarihi dai ya nuna cewa, bayan rasuwar jagoran mabiya darikar ta Kadiriyya Sheikh Nasiru Kabara a ranar 4 ga watan OKTOBA a alif da dari tara da casa’in da shida (1996) sai dansa da ya gaje shi sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya ci gaba da gudanar da bikin kamar yadda aka saba.
A cewar jagororin darikar ta Kadiriyya ana kuma gudanar da maukibin ne domin tunawa da ranar da aka haifi Sidi Abdulkadir Jilani wanda shine ya kafa darikar ta kadiriyya wanda suke tafiya zuwa masallacin Kamzu dake kan titin Katsina suna gudanar da yabo da Kasidu har suje wajan.
Kuma ya yin futar tasu mabiya Kadiriyya suna zuwa makabartar da aka binne Sheikh Nasiru Kabara domin gudanar da addu’a a gare shi da sauran mamatan dake wajan.
A wannan maukibin na bana wanda shine karo na 69 shugaban darikar ta kadiriyya, yayi kira ga jama’a da su rungumi dabi’ar zaman lafiya wanda hakan zai taimaka wajan ci gaban kasa.
Sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya kuma ce, yana da kyau shugabanni su rika mayar da hanakali wajan magance matsalolin sace-sacen kananan yara da ke wakana a jihar Kano da wasu sassan kasar nan.
Haka zalika jagoran mabiya darikar ta Kadiriyya ya bukaci hukumomi da su dinga sanya idanu wajan ganin an hukunta masu laifin da aka kama domin zama izina ga na gaba.
Bikin maukin na bana dai ya samu halartar wasu daga cikin jagororin darikar ta kadiriyya na kasashen duniya musasamman wadanda suka zo daga kasar Sudan.
labarai masu alaka:
Kano9: Ina rokon mahukunta su magance satar yara -Sheikh Kariballah Kabara
Limamin jumu’a a Kano yayi Allah-wadai da “Black Friday”