Connect with us

Labarai

Shettima ya buƙaci jihohi su daina dogaro da gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin lantarki

Published

on

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci gwamnatocin jihohin kasar nan da su daina dogaro da gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin wutar lantarki, su kuma yi amfani da dokar wutar lantarki ta shekarar 2023 wajen kafa kasuwannin wutar lantarki na jihohinsu.

 

Kashim Shettima, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki kan dokar wutar lantarki ta 2023, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

 

Mataimakin shugaban ƙasar, wanda mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya wakilta, ya ce burin Najeriya na gina tattalin arziƙin masana’antu ba zai cika ba matuƙar ba a samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ’yan kasuwa, gidaje da cibiyoyin gwamnati ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!