Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙudirin dokar kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Rogo

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Ƙaramar Hukumar Rogo.
Wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa labarai na Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar.
Sanarwar ta ce, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano ne ya jagoranci ƙudirin dokar kafa kwalejin, wanda majalisar ta amince da shi.
Ya ce, Ƙudirin dokar ya tanadi kafa kwalejin ne a Rogo, domin ta kasance cibiyar koyar da kimiyya da fasaha a jihar.
You must be logged in to post a comment Login