Connect with us

Labarai

Ganawar Shugaban APC da Sanata Rufai Hanga ta janyo ce-ce-ku-ce

Published

on

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Hanga, a wata ganawa da aka gudanar a boye ranar Lahadi.

 

A cewar Yilwatda, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan hadin kai, zaman lafiya da ci gaban jihar Kano, inda ya ce shugabanni na da alhakin tattaunawa da hada kai domin tabbatar da ci gaban dimokuradiyya da fifita muradun al’umma.

 

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaben 2027. Sanata Rufai Hanga, wanda ke cikin jagororin NDC a Kano, ya rasa tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya bayan jam’iyyar ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, tikitin takara. Wannan ya kara haifar da rade-radin cewa Hanga na iya sake nazarin makomarsa ta siyasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!