Kasuwanci
Shigowar yan China harkar jari bola ne ya kawo mana nakusu a kasuwancin mu – kungiyar jari bola
Ƙungiyar ƴan jari bola ta kasa tace rashin masana’antun da suke sayan kayansu a arewacin Najeriya ne yasa suke kai wa kudu.
Ƙungiyar ta kuma ce, a yankin kudu ne ƴan kasashen china da indiya suka bude masana’antun da ake sarrafa kayayyakin da suke tarawa.
Shugaban ƙungiyar kwamared Salisu Ali Yarima ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na freedom Radio.
Salisu Yarima ya kuma ce lura da ana samun kayan jari bola da yawa a Kano saboda yawan al’umma yasa yan kasashen zuwa su bude cibiyoyin tattara kaya maimakon masana’antu.
“Muna asarar makudan kudade wajen yin sufuri daga arewa zuwa kudu domin sayar da kaya sai dai kuma idan wadannan masana’antu sun sarrafa kayayyakin arewa suke kawowa su sayarwa kamfanoninmu na gida”.
“Fuskantar ana samun kayan sarrafawa a Kano yasa suka fara shigowa Kano suna kafa cibiya wanda hakan ya fara durkusar da mu”.
Yarima ya kuma ce a shekarun baya suna amfani da injinan da suke bukatar ma’aikata da yawa amma yanzu kasashen na samar da injin da kanyi aikin da mutane 50 za suyi hakan yasa matasa suka rasa aikin yi a arewacin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login