Rahotonni
Shin kun san muhimmancin abun kashe Gobara-Fire Extinguisher
Iftila’in gobara dai kan faru a lokuta daban-daban a cikin jama’a, musamman a lokaci na dari {Sanyi}wanda ke sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
A wani mataki na yin shirin ko-ta-kwana, da daukar matakin gaggawa ta sanya kwararru suka kirkiro abin kashe gobara cikin gaggawa don yin rigakafi na kasha wuta da aka fi sa ni da Fire Extinguisher.
Muhimmancin abin kashe gobara na Fire Extinguisher ba zai misaltu ba, musamman ma a cikin gidaje da asibitoci da masana’antu, har ma a cikin ababen hawa ciki da motoci da kasuwanni da sauran wurare.
Sai dai jama’a da yawa daga cikin mutane ba su san muhimmancinsa ba, a gefe daya kuma ba sa tanadar sa don ajiyewa a kusa da su a matsayin kariya a matakin farko daga hadrin gobara.
Labarai maus alaka.
Kano: Gobara da hadura sun hallaka mutane da dama a watan da ya gabata
Gobara ta tashi a makaranta kwanan dalibai ta Kanwa
A lokuta da dama amfani da abin kashe gobarar kan taimaka wajen rage asarar da ake tafkawa a lokacin gobara.
A ta bakin kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Sa’id Muhammad Ibrahim, a wata zantawar sa da wakiliyar Freedom Radio, Binta Ibrahim Yakasai, yace muhimmancin abin kashe gobarar na da yawa kwarai da gaske, musamman ma a lokacin da gobara ta afku.
Sa’id Muhammad ya kuma ja hankalin al’umma da su tanadi abin kashe gobara a duk inda suke, sannan kuma su rinka sabunta shi da zarar wa’adinsa ya kare, don kare rayuka da dukiyoyinsu.
You must be logged in to post a comment Login