Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Shirin bunkasa noma da kiwo na jiha zai hada kai da cibiyoyin bincike

Published

on

 

Shirin bunkasa Nima da kiwo na jihar Kano, wato Kano state Agro Pastoral Development Project (KAPDP), zai samar da yadda za’a bunkasa samar da Madara ta cikin gida don fadada tattalin Arziki, a cewar shugaban Shirin Malam Ibrahim Garba Muhammad , wanda yace cigaba da shigo da Madara daga kasashen Ketare yana kawo koma baya wajen tattalin Arziki kasar nan, kasancewar ana kashe sama da dalar Amurka Biliyan 1, akan shigo da Madara da danginta, duk shekara .

Malam Ibrahim Garba Muhammad, ya bayyana hakan ne a yau, lokacin da yake karbar shugaban Hukumar Bincike da Bunkasa Albarkatun Kasa wato Raw Materials Research and Development council of Nigeria ,RMRDC, na jiha Malam Hambali Muhammad.

Ibrahim Garba Muhammad , ya ce “Gibin da ake dashi na samar da Madara da bukatar ta na kara karuwa don haka , zamu yi amfani da Shirin don samar da wadatacciyar Madara tare da samar da ita ga kasashen waje”.

 

Labarai Masu Alaka.

Shirin bunkasa noma zai hada kai da cibiyar NAPRI don samar da abincin dabbobi

Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi

” Don haka muka samar da tsare -tsare na shirin yin bayen Shanu, samar da wajen Adana Madara 200, shukar ciyawar kara Madara ga Shanu da bada horo ga makiyaya don samar da Madara da Nono mai kyau da tsafta , don haka a shirye muke mu hada kai daku don samun shawarwari wajen bunkasa shirin tare da samun Nasara”.

A nasa jawabin shugaban Hukumar Bincike da bunkasa Albarkatun Kasa na jiha RMRDC, Malam Hambali Muhammad , ya ce makasudin zuwan su shi ne don hada kai da shirin tare da tafiya a tsira tare na cigaba.

“Hukumar mu an umarce ta , data bunkasa tare da tallata kayan da ake samarwa cikin gida , don haka zamu yi aiki tare don cigaba mai dorewa “.

A sanarwar da jami’in yada labarai na shirin ya sakawa hannu da aka rabawa manema labarai Aminu Kabir Yassar , ya fitar , ta ambato Malam Hambali Muhammad , ya bukaci shirin da ya yi amfani da binciken hukumar don cimma manufofin sa akan harkokin Noma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!