Labarai
Shirin N-Powar ya sauya rayuwar matasan kasar nan – Minista
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin N-Power ya canja rayuwar matasan kasar nan musamman ma ta bangaren samar da aikin yi.
Ministan jin kai dakile ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan lokacin da take jawabi a yayin taron bikin cikar ta shekara daya a ma’aikatar wanda ya gudana a Abuja.
Hajiya Sadiya ta kara da cewa ma’aikatar ta ta tattara bayanan wadanda suka samu nasar samun aiki karkashin shirin na N-Power a karon farko da na uku su kimanin dubu dari da tara da dari takwas da ashirin da uku, inda tuni suka dogara da kan su bayan kammala aiki karkashin shirin N-power.
Ta kara da cewa ko a wannan karon na yin rijistar shirin gwamnatin tarayya ta kara wa’adin mako biyu don baiwa matasa damar yin rijistar shiga shirin wanda a yanzu adadin wadanda suka nemi aikin a karo na uku ya kai sama da miliyan biyar.
Hajiya Sadiya ta kuma ce, ma’aikatar ta za tayi kokari wajen tabbatar da baiwa wadanda suka cancanta damar samun aiki a karkashin shirin na N-Power na wannan karon.
You must be logged in to post a comment Login