Labarai
Shirin tura jami’an sintirin dazuka na ci gaba da karɓuwa

Shirin tura jami’an sintirin dazuka na ci gaba da karɓuwa a sassan kasar nan, inda jihohin Kebbi, Gombe, Kwara, Kaduna, Edo, Imo, Bayelsa da Anambra suka fara faɗaɗa ayyukan tsaro a karkashin shirin da gwamnatin Tarayya ke marawa baya domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Wannan sabon yunƙuri ya biyo bayan amincewar Shugaban kasa Bola Tinubu na ɗaukar sabbin jami’an sintirin dazuka 1,000 bayan hare-hare da sace-sacen mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne suka aikata a jihohin Oyo da Kwara.
A jiya Lahadi ne dai Shugaba Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro tare da tabbatar da ceto dukkan mutanen da ke hannun masu garkuwa da su a faɗin ƙasar nan.
A Jihar Kebbi kuwa, an tura sabbin jami’an sintirin dazuka 819 bayan kammala horas da su.
Mataimakin Gwamnan jihar, Umar Tafida, ne ya bayyana hakan a wajen bikin yaye jami’an da cewa an tura su ne domin hana ƙungiyoyin masu aikata laifuka amfani da dazuka a matsayin mafaka.
You must be logged in to post a comment Login