Labaran Kano
Shiyyar Kano da kewaye za su amfana da wutar lantarki – KEDCO
Kamfanin rarraba hasken lantarki na Kano KEDCO yace abokan huldar sa dake shiyyar Kano da kewayan ta za su fara amfana da karin wutar lantarki bayan da kamfanin ya inganta harkokin sa.
Hakan ya biyo bayan nasarar da kamfanin TCN yayi na kammala gyara a layin samar da wuta na Shiroro-Mando wanda yake samar da wuta ga alummar jihar Kano da kewayen sa.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun kamfanin na KEDCO Ibrahim Sani Shawai ya sanyawa hannu.
Sakamakon wannan aikin da kamfanin na TCN yayi na kara yawan wutar da yake samar wa daga karfin MW 150 zuwa MW 200 a kullum kuma hakan zai cigaba in dai har ana samun cigaba daga tashar wutar.
Labarai masu alaka :
Kungiyar ma’aikatan lantarki sun garkame ofishin KEDCO
Kungiyar ma’aikatan lantarki ta janye yajin aikin data tsuduma
Kamfanin TCN ta tallata gwanjon jirage masu saukar ungulu
Akan haka ne Kamfanina KEDCO yake yabawa abokan huldar sa saboda kyaky-kyawar fahimtar da suka yi, yayin da suka bukaci kwastomin su kan su ci gaba da biyan kudin wuta akan lokacin mussaman ma a shiyar Kano da Katsina da kuma Jigawa.
You must be logged in to post a comment Login