Wasanni
Shooting Stars ta nemi afuwar magoya bayanta
Sunusi Shuaibu Musa
Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars ta bukaci magoya baya da su ci gaba da basu hadin kai da goyon baya, bayan da kungiyar ta tashi kunnen doki da kungiyar kwallon kafa ta Remo Stars a ranar Lahadi a wasan hamayya na kudancin yamma.
Kungiyar ta shooting Stars bata taba samun nasara kan takwarorin nasu ba a gasar Firimiya Najeriya.
Magoya bayan kungiyar sun nuna damuwarsu yayin wasan da ya gudana a filin wasa na Lekan Salami dake Ibadan.
You must be logged in to post a comment Login