Labarai
Shugaba Tinubu zai yi jawabi kan dawowar Demokuradiyya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi ga zaman haɗin gwiwar Majalisar Dattawa da ta Wakilai a ranar 12 ga Yuni, a wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 27 da dawo da mulkin dimokuraɗiyya a kasar nan.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin ministoci da aka ɗora wa alhakin shirya bukukuwan a Abuja. Ya ce jawabin shugaban ƙasa zai kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su gudana a ranar.
Akume ya bayyana cewa ranar Dimokuraɗiyya wata dama ce ta tunawa da sadaukarwar waɗan da suka yi gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya, musamman marigayi Moshood Kashimawo Abiola da sauran jaruman gwagwarmayar 12 ga Yunin 1993.
A cewar sa, gwamnatin tarayya za ta yi amfani da bikin wajen nuna nasarorin da ta samu wajen ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da bunƙasa ci gaban ƙasa duk da ƙalubalen tattalin arziki.
Daga cikin shirye-shiryen bikin akwai taron manema labarai na duniya a ranar 4 ga Yuni, addu’ar Juma’a ta musamman a ranar 5 ga Yuni, ibadar coci ta haɗin mabiya addinai a ranar 7 ga Yuni, da kuma lacca ta ranar Dimokuraɗiyya a ranar 9 ga Yuni. Haka kuma za a gudanar da shirye-shirye na matasa da mata a ranar 10 ga Yuni.
A ranar 12 ga Yuni, shugaban ƙasa zai yi jawabi ga al’umma, sannan za a kammala bukukuwan da liyafar maraice ta ranar Dimokuraɗiyya.
You must be logged in to post a comment Login