Siyasa
Shugaba Buhari ya amince da sauyawa wasu manyan sakatarori hudu wuraren aiki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sauyawa wasu manyan sakatarori hudu wuraren aiki, inda aka mayar da su ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mrs Winifred Oyo-Ita ce ta bayyana hakan, a wata sanarwa da ta fitar yau a Abuja.
Sanarwar ta ruwaito cewa daga cikin manyan ma’aikatan da aka sauyawa wuraren aikin sun hadar da babban sakataren ma’aikatar tama da karafa Alhaji Mu’azu Abdulkadir, wanda yanzu haka aka mayar da shi babban sakataren ma’aikatar lura da harkokin noma da raya karkara ta tarayya.
A cewar sanarwar babbar sakatariyar ofishin sakataren gwamnatin tarayya wato Mrs Georgina Ehuria, an mayar da ita ma’aikatar tama da karafa a matsayin babbar sakatariya, yayinda babban sakataren sashen ayyukan na musamman a ofishin shugaban ma’aikata ta tarayya Aliboh Leon aka mayar da shi ma’aikatar muhalli.
Sanarwar ta bayyana cewa Alhaji Sulaiman Mustapha na ofishin kwarewa a ayyukan gwamnati an mayar da shi ma’aikatar lura da harkokin kasashen waje a matsayin babban sakatare.
Kamar yadda shugabar ma’aikatan ta bayyana sanarwar na umartar dukkanin sakatarorin da su mika takardun kama aikin da aka basu kafin ranar ashirin da takwas ga watan da muke ciki na Satumba, domin fara aiki a wuraren da aka tura su a kan lokaci.