Manyan Labarai
Shugaba Buhari ya bukaci a baiwa ‘yan Najeriya mazauna Africa ta kudu kariya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci kasar Africa ta kudu da ta kare rayuka da dukiyar ‘yan kasashe da dama da ke zaune a kasar ta Afirka ta kudu, sakamakon cin zarafin da suke fuskanta musamman a birnin kasar Johannesburg.
Shugaba Buhari ya bukaci hakan ne a yau yayin wata doguwar tattaunawa da ya yi da shugaban kasar Cyril Ramaphosa kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.
Ana dai sa ran tattaunawar tasu zata kawo karshen cin zarafi da tada rikice-rikicen da ake yi a yankunan da ‘yan kasashe da dama ke zaune a kasar musamman ma ‘yan Najeriya da suka sha fuskantar matsaloli.
Rahotonni sun bayyana cewa, ko a watan Satumban da ya gabata an balle wasu manyan shagunan kayan masarufi tare da yi musu sata da kuma banka musu wuta a Johannesburg, wanda kuma dukkan su mallakin ‘yan kasashen ketare ne.
Ko a kwanakin baya rikicin kasar ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 12 baya ga daruruwan mutane da suka yi gudun hijira sanadiyyar rikicin.
Shugaba Buhari ya kuma yi Allah wadai bisa harin mayar da martani da wasu suka kai kan wuraren kasuwanci mallakar ‘yan kasar ta Afika ta kudu a wasu sassan Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar rufe wuraren kasuwancin su a jihohi da dama.
A nasa jawabin, shugaba Cyril Ramaphosa,ya nanata bada hakuri bisa hare-haren bayyana rashin jin dadinsa kan ayyukan ta’addancin da ya auku a kasar yana mai cewa gwamnatinsa ta yi nadamar faruwar hakan.