Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya su kara hakuri dangane da matsalolin tsaro da ke addabar kasar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar Najeriya kara hakuri dangane da matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na kasar nan, Kasancewar gwamnatin sa na aiki ba dare ba rana tare da dukkanin hukumomin tsaro, domin kawo karshen ta’addancin.
Shugaba Buhari ya yi kiran ne yayin da yake yin Alla-wadai da kisan gillar da wasu ‘yan bindiga suka yi wa mutane da dama a ciki da wajen kauyen Gandi da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto, ciki har da wani Hakimi.
Cikin sakon da ya aike ta hannun kakakin sa Malam Garba Shehu, Shugaban Buhari ya bayyana mamaki da kaduwa dangane da yadda masu kisan gillar ke hallaka wadanda basu ji ba basu gani ba, ba tare da dalilin komai ba.
Buhari ya kara da cewa gwamnatin sa za ta tabbatar cewa ta gano tushen wannan matsala ta hare-haren ‘yan bindiga musamman ma wajen gano wadanda ke tallafawa ta’addancin a boye.
A makon da ya gabata ne, yayin wata ziyara da ya kai garin Munguno a jihar Borno, shugaba Buhari ya zargi wasu gurbatattun ‘yan siyasa da haddasa matsalolin tsaro a sassan Najeriya, domin cimma manufofin siyasa, musamman shafawa gwamnatin sa bakin fenti.