Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin asusun tallafin kula da harkokin lafiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da shirin asusun tallafin kula da harkokin lafiya wato Basic Health Care Provision Fund, wanda aka sanya shi cikin kunshin kasafin kudin bana.
Gwamnatin tarayya dai za ta rika ware kaso daya na dukkan arajin da ake samu da kuma gudunmawa daga kungiyoyin ba da tallafin lafiya a cikin asusun kula da tallafin harkokin lafiyar.
Majalisun dokokin tarayyar kasar nan dai tun a shekarar dubu biyu da goma sha hudu suka yi dokar asusun tallafin kula da harkokin lafiya sai dai sai a wannan karon gwamnatin tarayya ta sanya shi cikin kasafin kudi.
Da ya ke kaddamar da shirin shugaban Buhari wanda ministan kasafin kudi da tsare-tsare Sanata Udoma Udo Udoma ya wakilta, ya ce gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan hamsin da biyar da miliyan dari daya don fara shirin asusun tallafin kula da harkokiin lafiya
Haka zalika, gidauniyar fitaccen attajirin nan na Amurka Bill and Melinda Gates Foundation ta ba da dala miliyan biyu domin fara shirin asusun tallafin kula da harkokin lafiyar.
Sauran wadanda suka yi alkawarin ba da gudunmawa cikin asusun tallafin kula da harkokin lafiyar, sun hada da: Cibiyar ba da tallafi ta duniya wadda ta yi alkwarin dala miliyan ashirin, yayin da hukumar bunkasa kasashe ta burtaniya (DFID) ta ce za ta ba da fan miliyan hamsin a cikin asusun.