Labarai
Shugaba Buhari yayi alkawarin kamo bakin zaren sabanin tsakanin babban sufeto da Bukola saraki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya alkawarta daukar matakan da suka dace domin kamo bakin zaren dangane da wani sabani da ya bullo tsakanin babban Sufeton ‘yan-sandan kasar nan da kuma shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan jiya lokacin da ya ke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, bayan kammala wata ganawar sirri da shugaban kasa, da tawagar Sanatoci 10.
Ahmad Lawan ya ce shugaba Buhari ya sha alwashin warware matsalolin da su ka addabi bangaren zartaswar da na Majalisa baya ga waccan matsala da ta kunno kai tsakai babban Sufeton ‘yan-sandan kasar nan da Sanata Bukola Saraki.
Haka zalika ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ganawar za ta haifar da ‘da mai ido, wanda kuma zai janyo ci gaban kasa ta fannoni da dama.
A ranar 9 ga watan Mayun da mu ke ciki ne majalisar ta kasa kuri’ar yanke kauna ga babban Sufeton ‘yan-sandan bayan da ta ayyana shi a matsayin makiyin Dimokradiyya sakamakon kin mutunta gayyatar da su ka yi ma sa.
A makon jiya ne dai Saraki ya zargi babban Sufeton ‘yan-sandan Ibrahim Idris da yunkurin shafa masa kashin kaji tare da gwamnan Jihar Kwara Abdulfatah Ahmad kan zargin kisan kai.