Labarai
Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da Emefiele kan matsalar karancin kudi a Nijeriya
Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da Shugabanin Kungiyar gwamnoni ta kasa Aminu Waziri Tambuwal, da Shugaban Kungiyar jam’iyar APC Atiku Bagudu kan matsalar karancin sabbin takardun kudin da ake fuskanta.
Daga cikin waɗanda suka halarci zaman har da gwamnan Babban Bankin ƙasar Godwin Emefiele da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar Abdulrasheed Bawa da kuma babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar Janar Lucky Irabor.
An yi ganawar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Da farko an tsara zaman da ƙungiyar gwamnonin ƙasar, to sai dai daga baya an soke zama da duka gwamnonin sakamakon wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Bayyanar gwamnan Babban Bankin a ganawar alama ce da ke nuna cewa an tsara zaman ne domin tattauna batun matsalar ƙarancin kuɗi, da ke fuskantar suka daga ‘yan ƙasa, ciki har da gwamnonin ƙasar.
A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasa ya gana da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, inda wasu daga cikin gwamnonin suka yi kira ga shugaban ƙasar da ya shiga tsakani domin bayar da dama a ci gaba da amfani da tsoffi da abbin takardun kuɗin a faɗin kasa.
To sai dai rahotonni sun ce shugaban ƙasar ya yi watsi da buƙatar kasancewar kotu ta haramta wa gamnati sake ƙara wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Wasu majiyoyin a fadar shugaban ƙasar sun tabbatar da cewa shugaban ƙasar na kaffa-kaffa, kada ayi masa kallon mai watsi da dokoki.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login