Labarai
Shugaba Buhari:Ya zargi yan bindiga dadi da yin kisa a matsayin fulani makiyaya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba wasu bane masu yin kisa da sunan Fulani makiyaya face yan bindigar da tsohon shugaban kasar libiya Mua’ammar Gaddafi ya raina.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a jiya bayan da Archbishop Canterbury Justine Welby ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin tarayya da ke birnin London.
A cewar sa yan bindigar sun tsere ne da ga kasar ta Libya inda suka fantsama a Najeriya da sauran kasashen Afrika bayan mutuwar Gaddafin.
Shugaban Buhari ya ce koda kisan da ake zargin Fulani makiyaya sun yiwa mutane goma sha uku a jihar Benue da Nassarawa a ranar Talatar da ta gabata na da alaka da yan bindigar.
Da yake maida jawabi kan tambayar da Archbishop ya yiwa shugaban kasar kan batun rikicin Fulani makiyaya da manoman da ke faruwa a wasu bangarorin kasar nan, shugaban Buhari ya ce rikicin tsohon al’amari ne da ya kwashe shekara da shekaru ana yin sa ba wai yanzu aka soma ba.
Ya ce tun tuni ake gwabzawa sai dai a wannan lokaci ne al’amarin ya ta azzara fiye da kowanne loaci.